Babu Inda Na Ce Za A Kulle Wanda Bai Yi Katin Ɗan Ƙasa Ba – Pantami

Ministan Sadarwa da raya tattalin arziki na Digital Dakta Isa Ali Pantami, ya karyata rahoto dake yaduwa cewa yace duk wanda ba shi da lambar katin zama dan kasa (NIN) zai ci zaman gidan yari na tsawon shekaru 14.

Pantami ya bayyana cewa ko sau guda bai ambaci hukuncin daurin shekaru 14 ba. Kawai abinda ya fadi shine an kafa hukumar NIMC na tsawon shekaru 14 yanzu.

Hakazalika ya kalubalanci wata kafar jaridar da ta wallafa labarin cewa ta saki bidiyon inda ya fadi hakan.

“Wadannan mumunan fassara ne. Pantami bai ambaci daurin shekaru 14 ba. Amma yace NIMC ta kwashe shekaru 14 da kafa ta, tun 2007”.

“Tun da yan jarida sun shaida jawabin, kamata yayi a saki bidiyon ga mutane su gani,” ya bayyana a shafinsa na Tuwita.

Labarai Makamanta