Babu Hannumu A Dakatar Da Mukabalar AbdulJabbar Da Malamai – Ganduje

Gwamnatin Kano ta yi amanna da hukuncin kotun majistare ta jihar wacce ta hana yin mukabala tsakanin malaman jihar da Sheikh Nasiru Kabara.

A ranar Juma’a, 5 ga watan Maris ne kotun ta zartar da wannan hukunci, ana saura kwana biyu kafin gudanar da mukabalar da mutane ke ta zuba ido.

Hukuncin kotun ya nemi a tsaya kan hukuncin da kotu ta zartar tun a ranar 8 ga watan Fabrairu, wanda ya hada da haramtawa Sheikh Kabara yin wa’azi a jihar.

Kwamishinan labarai na jihar Kano, Muhammadu Garba, ya shaida wa sashin Hausa na BBC cewa bayan zantawa da gwamnati ta yi da bangaren shari’a, sun gamsu da wannan hukunci.

Ya ce saboda haka, an fasa yin mukabalar da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi, 7 ga watan Maris.

Da aka tambaye shi kan zargin da ake yi na cewa da hannun gwamnatin Kano a shigar da karar da aka yi domin hana zaman mukabalar, saboda sarkin Musulmi ya nuna rashin amincewarsa da hakan, ya ce wannan zargi kanzon kurege ne.

Ya kara da cewa ko da an daukaka kara daga baya wata kotun ta ce a gudanar da zaman, sai Gwamnatin Kano ta sake yin nazari kafin duba yiwuwar yin hakan.

A nashi bangaren, daya daga cikin lauyoyin Sheikh Kabara, Barista Tabiu Shu’aibu Abdullahi, ya ce su a iya saninsu wannan zama na nan, cewa babu wani waje da kotu ta fito karara ta hana yin mukabalar.

“Abun da muka fahimta a wannan hukunci shine kotu ta ce a ci gaba da aiki da hukuncin da aka zartar a ranar 8 ga Fabrairu. Cewa ta haramtawa Abduljabbar yin wa’azi da kuma yin kalaman tunzurawa, da rufe masallaci da makarantu, amma babu wani waje da tace kada a yi mukabalar da aka shirya.”

Ya jaddada cewa ko kadan hukuncin da kotu ta zartar bai da nasaba da yin mukabalar, balle ma har a ce za a fasa ta.

Barista Rabiu ya kuma ce ko da dai wasu na son fakewa da hana Kabara yin wa’azi da kotu ta yi, “to a kwana da sanin cewa ba wa’azi za a yi da shi ba, ita Gwamnatin Kano cewa ta yi tattaunawa za a yi.”

A baya mun ji cewa, wata kotun Majistsare da ke zamanta Gidan Murtala a jihar Kano ta bada umurnin dakatar da mukabalar da gwamnatin jihar ta shirya yi tsakanin Abdul-Jabbar da malaman Kano a ranar Lahadi 7 ga watan Maris.

Alkalin kotun, mai shari’a Muhammadu Jibrin ya yanke hukuncin dakatar da mukabalar sakamakon bukatar da wani lauya mai zaman kasan, Barrister Ma’aruf Yakasai ya shigar wa kotun.

Yakasai ya bukaci a dakatar da yin mukabalar ne saboda hakan ya saba umurnin da kotu ta bayar a baya na hana Sheikh Abdul-Jabbar yin karatu da saka karatunsa a kafofin watsa labarai na jihar Kano.

Labarai Makamanta