Babu Gwamnati A Najeriya – Gana

“Tabbas abubuwa sun dagule, komai ya sukurkuce a Najeriya, babu wani abu dake tafiya daidai, sakamakon yadda Shugabancin ƙasa ke ya shiga ruɗani, lallai babu Shugabanci a wannan kasa tamu Najeriya”

Kalaman tsohon Ministan yaɗa Labarai, Farfesa Jerry Gana kenan yayin da yayi wankan tsarki ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP, tare da magoya bayansa masu yawa a ranar Laraba.

A watan Maris ɗin 2018, Gana, mamba na kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya fice ya koma jam’iyyar SDP, bayan lashe wasu ‘yan shekaru Gana ya shelanta dawowa jam’iyyar a ranar Laraba.

Yayin da ya ke yi wa magoya bayansa jawabi a mahaifarsa dake Bida, Jihar Neja wurin bikin tarbarsa, Gana ya ce kasar na nutsewa kuma tana bukatar taimakon gaggawa.

Farfesa Gana ya ƙara da cewar “Yau ba ranar yin lakca bane. Ba ranar kamfen bane. Muna son muyi murnar cewa mun dawo mun haɗe wuri guda; kuma za muyi aiki tare yadda ya kamata sannan muyi yaƙin neman zaɓe gadan-gadan.

“Akwai Gwamnati a jihar Neja? Domin mutane da yawa ba su sani ba, ko a tsakiya? A matakin tarayya, ba mu da gwamnati.”

Tunda farko shugabannin jam’iyyar daga mazaɓu uku sun bawa magoya bayan PDP tabbacin cewa sun shirya karɓe jihar Neja su ceto jihar daga hannun APC da ta lalata al’amura.

Labarai Makamanta