Babu Gaskiya A Labarin Zan Koma APC – Kwankwaso

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana mai gamsarwa game da rade-radin da ake ji na cewa zai sauya sheka daga Jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

A wata hira da Gidan Rediyon DW Hausa tayi da shi a ranar Laraba, Rabiu Musa Kwankwaso yace babu gaskiya a jita-jitar da ke faman yawo a gari. Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi mulki sau biyu a jihar Kano, yace a halin yanzu bai yi wani zama da wasu a kan shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki ba.

A cewar Sanata Kwankwaso, ba yau aka saba yada irin wannan jita-jita ba, yace bini-bini a kan fito ana karyar wai yana shirin ficewa daga jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa APC.

“Maganar canza-sheka, babu ita. A yanzu dinnan ba na magana da wasu mutane na cewa zan koma (zuwa jam’iyyar APC).”

Amma tun kafin wannan lokaci, mutane suke ta yin jita-jita. Amma duk lokacin da jita-jitar ta taso, sai ka ga mutane sun yarda.” “Sai a ce ‘Ai Kwankwaso gobe zai koma, rana irinta yau zai koma, wata mai zuwa zai koma. Idan an zo an wuce, sai a sake shigo da wata.”

Har ila yau, DW tayi wa tsohon Ministan tsaron tambaya ko ya na da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, inda yace bai kai ga yanke shawara ba.

“Ba mu gaggawa, sai an yi Nazari, sai an taba mutanen da ya dace (masu hakki a kan al’amarin.” “Idan Allah ya kai mu wannan lokaci, idan Allah ya yarda za mu sanar da ku game da matakin da Kwankwaso zai dauka game da abin da ya shafi zabe na 2023.”

Labarai Makamanta