Babu Gaskiya A Labarin ‘Yan Bindiga Za Su Kai Hari Zariya – Gwamnatin Kaduna

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta karyata jita-jitar da ke cewa wasu ‘yan bindiga suna shirin kai hare-hare Zaria.

Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya fitar ranar Laraba ya nemi mutanen birnin na Zaria da su yi watsi da jita-jitar yana mai cewa ba su da kanshin gaskiya.

“An jawo hankalin gwamnatin Kaduna kan wani sako da ake watsawa sosai da ke ba mutane shawarar cewa su guji shiga ko fita daga Zaria, wanda ke ikirarin cewa akwai daruruwan ‘yan bindiga a yankin Dumbi da Jaji a kan hanyar Zaria.

Gwamnatin Jihar tana mai karyata wannan sako, kuma tana umartar mutane su yi watsi da shi baki daya,” a cewar sanarwar.

Ta kara da cewa ana yada sakon ne domin a tayar da hankulan jama’a, tana mai tabbatar wa mazauna yankin da matafiya cewa babu wata matsala a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Labarai Makamanta