Babu Gaskiya A Labarin Na Koma APC – Jonathan

Labarin dake shigo mana daga ofishin Tsohon Shugaban Kasa Jonathan na bayyana cewar tsohon shugaban Goodluck Ebele Jonathan ya musanta cewa ya koma jam’iyya mai mulki ta APC.

A ranar Laraba, wani rahoto ya bazu a dandalin sada zumunta cewa tsohon shugaban kasar ya nuna sha’awar yana son ya fice daga jam’iyyar PDP ta adawa zuwa APC mai mulki.

Mai magana da yawun Jonathan ya karyata rahoton a martaninsa, Ikechukwu Eze, mai magana da yawun Jonathan ya ce rahoton labarin kanzon kurege ne. Eze ya ce: “Rahoton ba gaskiya bane.

“Idan har ya sauya sheka zuwa wata jam’iyyar za a sanar ta kafar da ta dace.” Ya jaddada cewa mai gidansa bai nuna alama ko niyyar komawa jam’iyyar APC mai mulki ba. Ya kara da cewa: “Mutumin nan fa yanzu akwai wasu abubuwa masu muhimmanci da suka shige masa gaba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply