Babu Gaskiya A Batun Daukar Tubabbun ‘Yan Boko Haram Aikin Soja – Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban kasa a ranar Laraba ta karyata jita jitar da ake yada wa na cewa wai an dauki wasu daga cikin tubabbun yan Boko Haram aiki a Rundunar Sojojin Najeriya.

Wannan jita jitar ta bazu sosai a dandalin sada zumunta har ta kai ga wasu ‘yan Najeriya da dama sun fara shakku a kan shirin gwamnatin tarayya na sauya halin tubabbun yan ta’addan.

Jita jitar ta kara karfi jim kadan bayan Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya ce sojoji ne suka kai wa tawagarsa hari ba ‘yan Boko Haram ba.

Wasu yan Najeriya da dama a dandalin sada zumunta sun yi hasashen cewa akwai yiwuwar tubabbun ‘yan Boko Haram da ake ikirarin an dauka aikin soja ne suka kai wa Zulum hari.

Sai dai cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce wannan jita jitar ba gaskiya bace.

“Yana da muhimmanci mutane su san cewa babu wani Tubabben dan Boko Haram da ya shiga aikin soja a Najeriya cikin wadanda aka yaye a shirin sauya musu mummunar akidarsu kuma ba a shirin daukansu aikin sojan a nan gaba,” in ji shi.

Shehu ya yi karin haske game da shirin karbar tuban ‘yan ta’addan da suka mika wuya suka ajiye makamansu kuma suka shiga shirin na sauya hali da koyar da su sana’a. Ya ce Majalisar Dinkin Duniya, UN, da Tarayyar Kasashen Turai, EU da Kungiyar Yin Hijira ta Kasa da Kasa suna goyon bayan shirin.

Ba a daukan, “rikakkun yan ta’adda masu tsatsauran ra’ayi a shirin na sauya halayen,” a cewar Shehu.
Ya kara da cewa ana gudanar da bincike da tantancewa kafin a dauki tubabbun mayakan inda ya ce, “galibi wadanda aka tilasta musu shiga kungiyar ne ake dauka idan sun tuba da makamantansu …”.

Ya ce ana sa ran bayan an yaye su ba za su zama hatsari ga al’ umma ba kuma domin an cusa musu kishin kasa da kyawawan halaye. Shehu ya kara da cewa yana daga cikin hakkin alumma su karbe su muddin an tabbatar sun tuba.

Idan dai ba sun sake daukan makamai ba ya kamata shugabannin alumma su hada kai da hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa an daina kyamar su.

Har wa yau, ya ce gwamnatin Buhari mai nagarta ce kuma tana la’akari da halin da mutane ke ciki har da wadanda fitinar ta’adancin ya shafa da wadanda suka rasa ‘yan uwansu.

Labarai Makamanta