Babu Fargaba A Barazanar Boko Haram Na Kai Hari Abuja – Shugaban ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Baturen’yan Sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, yace babu wani abun tsoro kan barazanar da Boko Haram ta yi na kawo hari Abuja da Jihar Filato.

Kakakin hukumar yan sanda, Mr Frank Mba, shine ya bayyana haka a wani saƙo da ya fitar ranar Juma’a a Abuja, domin mayar da martani akan labaran da ake yaɗawa na cewar Boko Haram na barazanar kawo hari a birnin tarayya Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya gano wani rahoton sirri dake nuni da cewa, sufetan yan sanda ya ba kwamishinan ‘yan sanda na jihar Plateau da takwaransa na Abuja umarnin su ɗauki matakin da ya dace domin daƙile duk wani hari da za’a kawo yankunan su.

Ya buƙace su da su kare muhimman kayayyakin gwamnati dake yankin su biyo bayan gano shirin mayaƙan Boko Haram na kai hari. Sai dai kakakin hukumar yan sandan ya bayyana cewa wannan umarnin ba yana nufin akwai wata barazanar kawo hari a biranen biyu bane.

Yace an ba kwamishinonin biyu umarnin ne don su ƙara shiri wajen dakile duk wata barazanar kawo hari daga yan ta’adda a yankunan su. A cewarsa, anyi hakan ne don a ƙara tabbatar da doka a waɗannan garuruwan kuma a kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

“Umarnin ba yana nufin an san cewa za’a kawo hari a jihohin biyu bane kamar yadda wasu ke yaɗa wa.” inji kakakin yan sandan. Ya kuma roƙi mazauna waɗannan jihohin biyu su kwantar da hankalinsu, su cigaba da gudanar da ayyukan su na yau da kullum.

Labarai Makamanta