Babu Dan Bindigar Da Zai Saura A 2023 – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnatinsa zata kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga da ƙalubalen tsaro kafin wa’adinsa ya ƙare a 2023.

Buhari ya yi wannan furucin ne a fadar mai martaba Sarkin Musulmi dake Sokoto ranar Alhamis, yayin da ya kai masa ziyara, domin jajanta kisan da ‘yan Bindiga suka yi wa jama’a a jihar.

Shugaban ƙasan ya nuna tsantsar damuwarsa game da halin da mutane ke ciki a arewa maso yamma, inda ya ce baya iya runtsawa ya yi bacci.

“Abun damuwa ne matuƙa, al’umma ɗaya da al’ada iri ɗaya amma suna kashe junan su ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.” Shugaban ƙasa ya kuma tabbatar da cewa zai miƙa mulkin Najeriya bayan ya murkushe duk wata damuwa ta rashin tsaro da faɗuwar tattalin arziki.

Labarai Makamanta