Babu Dalilin Bincikar Tsoffin Shugabannin Tsaro – Fadar Shugaban Ƙasa

Ministan yada labarai da Al’adu na kasa, Lai Muhammad, ya ce babu bukatar gudanar da bincike ga tsaffin hafsoshin tsaro da aka sauke saboda a cewarsa ko wace ma’aikata tana da dokokin hukunta laifuka.

Ministan wanda ya bayyana haka lokacin da yake Magana a wani shirin talabijin ranar Talata, ya kuma caccaki masu kiran kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta bincike tsaffin hafsoshin, yana mai bayyana su a matsayin marasa kishin kasa.

A makon jiya ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin hafsoshin tsaron da suka maye gurbin tsaffin, saidai kuma jam’iyyar adawa ta PDP da sauran wasu ‘yan Nijeriya na ta kiran ganin an binciki tsaffin hafsoshin, kan matsalolin tsaron da suka ki ci suka ki cinye wa a kasar lokacin shugabannincinsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply