Babu Batun Sallama: Nnamdi Kanu Zai Girbi Abin Da Ya Shuka – Malami

A hirarshi da Muryar Amurka, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce maganar saki ko maganar shirin saki bata taso ba kamar yadda yake ta fuskar tsarin ma’amalar shari’a. Bisa ga cewarsa, ita wannan shari’a ko kuma wannan hukunci da aka yi kacokan ya dogara ko ya ta’allaka kan ma’amalar da ake da’awar cewa ainihin an kawo shi Najeriya ta karfin tsiya daga Kenya ba’a kan tsari na doka ba.

“Idan ma shi hukunci yana iya tsayawa ko ya inganta to kafin Nnamdi Kanu ya arce ya bar Najeriya akwai caji wanda yake wanzuwa wanda yake ingantacce gaban kotu, idan kana tunawa ya arce ya tsallake beli bayan an gurfanar da shi gaban kotu, kuma wadannan caji babu wani hukunci na kotu a kansu caji ne da ake bin bahasin su a gaban kotu,” in ji Malami.

Ya ce saboda haka idan ana maganar bayan ya arce yaje Kenya kuma akwai abubuwa wadanda suke gaban kotun tana dubawa kafin ya arce zuwa Kenya, saboda haka hukunci a kan daya daga cikin bangare da ke cikin al’ammuran da ke a gaban kotu zai zama wajibi ba zai zama wato yana aiki a kan sauran caje-caje wadanda suka gabaci kafin arcewarsa zuwa Kenya ba.

Ya kara da cewa, “idan kotu ta yi hukunci idan ba kotun koli ba ce, akwai dama ta daukaka kara, akwai damar ta warware hukuncin da kuma damarmaki daban da shari’a ta zo da su, kuma ala kulli hali a cikin wannan yanayi dai matsayin shi ne gwamnati za ta duba matsayin da take da shi ta fuskar shari’a ta kuma yiwa mutane adalci.”

Amma kamar idan za’a iya tunawa irin wannan shari’ar banbancinta da matsalar da ta haddasu a Amurka ta fuskar bin-Ladan kalilance idan har ma akwai banbanci, abin da ya faru a Amurka ta dauki matakin da ta dauka a kan bi-Ladan na zuwa wata kasa ma tatabbatar bin-Ladan bai wanzuwa ba shine kisa da ingiza mutane su yi kisa a kan Amurka da ‘yan kasa baki daya.

Labarai Makamanta