Babu Batun Karba-Karba A Kundin Tsarin Mulki – Gwamnonin Arewa

Gwamnonin kudu a wani taro da suka yi a watan Yuli sun nemi cewa, mulkin Najeriya ya koma yankin nasu a shekarar 2023.

Saidai a taron da suka yi a Kaduna, gwamnonin Arewa 19 sun mayarwa da na kudun martanin cewa mulki ba na karba-karba banr kamar yanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Gwamnonin sun ce ba za’a tursasa Arewa kada ta nemi shugaban kasa a shekarar 2023 ba dan kuwa kundin tsarin mulki ya bata damar yin hakan.

Sun ce duk da yake ana iya baiwa kudu damar yin mulki a shekarar 2023. Amma dai a zahiri gaskiya ba abune na dole-dole ba.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ne ya bayyana haka a sanarwar bayan taron da ya fitar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply