Babu Batun Karba-Karba A Kundin Tsarin Mulki – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 Alhaji Atiku Abubakar ya ce a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya babu wani tsari na karba-karba a ko wacce kujera.

Jigon na jam’iyyar PDP kuma Wazirin Adamawa ya yi wannan bayanin ne a wani taron da ya yi da kungiyar da ke kira a gare shi don ya sake tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023.

Kawo yanzu, Atiku bai riga ya bayyana kudirinsa na tsayawa takara ba, amma ya ce wani lokacin idan ya kalli kalubalen da kasar nan take fuskanta ya kan sake tunani akan ya tsaya takara ko ya fasa tsayawa.

“Shugabanci na Allah ne. Zaka iya ganin matashi mai karancin shekaru ya mulki kasa fiye da tsoho. “Don haka komai na Ubangiji ne, mu yi kokarin neman wanda ya tara duk halaye na kwarai don mu ba shi shugabanci.

“Ban taba ganin lokacin da kalubale ya yi yawa a kasar nan ba kamar yanzu. Wani lokacin ina kwance a gado na ina kokwanto idan zan yi takara. A rayuwa ta ban taba ganin Najeriya a wannan halin ba.”

Dangane da karba-karba, Atiku ya ce a kundin tsarin mulkin Najeriya babu inda aka haramta wa wani yanki takarar shugaban kasa. Ya ce babu wanda ba zai iya takara ba kuma babu wani batun karba-karba a yankunan Najeriya.

Labarai Makamanta