Babu Batun Cire Haruffan Ajami A Takardun Naira – Sanusi

Tsohon gwamnan babban bankin CBN, Muhammadu Sanusi II, ya fito ya yi magana game da jita-jitar cire rubutun Ajami daga takardun Naira, inda ya tabbatar da cewar labarin cire ajami a takardun kuɗin kanzon kurege.

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta an ji tsohon Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi II yana karyata rade-radin da ke yawo. Ganin har wasu malaman addini sun fara fashin-baki a kan lamarin alhali bai tabbata ba, Sanusi II ya yi kira ga malaman su daina aiki da jita-jita.

“Akwai maganganu da suke ta yawo a kan canza kudin Naira, na ji malamai dabam-dabam; ana zargin za a cire Ajami daga Naira. Nayi magana da ‘Yan CBN ina so in yi amfani da wannan dama, in tabbatarwa al’ummar Musulmi cewa babu gaskiya a cikin wannan maganar.

“A lokacin da aka fara maganar, mun yi magana da mutanen CBN Sun tabbatar mani da cewa babu wannan maganar. Da maganar tayi zafi, ni kai na, nayi magana da gwamnan banki Gwamnan babban banki ya tabbatar mani da cewa babu maganar cire Ajami daga kan Naira.

“Don Allah malamai a daina aiki da jita-jita, mun san malaman da ke magana, suna magana ne a kan abin da aka kawo masu ba tare da bincike ba.” Khalifan na Tijjaniya ya tunawa al’umma koyarwar addinin Musulunci game da yin bincike idan wani ya kawo labari, kafin a dauki mataki saboda nadama.

Labarai Makamanta