Babu Bambanci Tsakanin Musulmi Da Kirista A Bauchi – Gwamna Bala

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamnan jihar Bala Muhammed, ya bayyana cewa kiristoci suna da yanci kwatankwacin na yan uwansu musulmai, wanda ya kamata a girmamashi a faɗin Jihar Bauchi.

An ruwaito Gwamna Bala Muhammed na faɗin haka yayin da shugaban kungiyar kiristoci, (CAN), Rabaran Abraham Damina, ya jagoranci tawagar kiristoci suka kai masa ziyarar bikin Kirsimeti a fadar gwamnatin Jihar Bauchi ranar Asabar.

Gwamnan yace a baya an watsar da kiristoci a harkokin gwamnatin jiha, amma gwamnatinsa ta kara yawan su a cikin gwamnatinsa domin nuna musu ana tare. Da yan uwana musulmai da kiristoci duk daya ne, babu bambanci.

Haka nan kuma ya nuna gamsuwarsa da rawar da kiristoci ke taka wa a gwamnatinsa. “Daga zuwan mu, mun fahimci an jingine kiristoci gefe ɗaya amma muka jawo su a jiki, muka kara yawan kiristoci a gwamnatin mu.”

“Na yi farin ciki cewa a lokacin mu ne muka kara jawo kowa a jiki kuma muka kara samar da soyayya tsakanin mu. Sannan muka karya duk wani kokarin rarraba mu, wanda ya hana mu kallon juna a matsayin ɗaya.”

“Muna gina manyan coci-coci kamar yadda muke gina masallatai saboda mun gano cewa duka muna da yanci iri ɗaya kuma wajibi mu kiyaye muku yancin ku.”

Labarai Makamanta