Babu Alaka Tsakanina Da Shugaban ‘Yan Bindiga – Sanata Marafa

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ba ya da alaka da gawurtaccen dan bindigan nan, Abdulmuminu Moossa dake jihar Sokoto.

Sanatan ya bukaci ‘yan sanda, jami’an hukumar DSS da sauran jami’an tsaro da su gabatar da rahoton da zai nuna alakarsa da Moossa, kamar yadda wadanda ya kira da sunan maƙiya ke yaɗawa.

A wata takarda wacce ofishin kamfen din sanatan ya saki a ranar Juma’a, ya ce lokaci ya yi da ya kamata jami’an tsaro su jajirce wurin yin bincike akan matsalar tsaron kasar nan.

“A rahoton, wanda ake zargin Abdulmuminu Moossa, dan asalin jamhuriyar Chadi, ya bayyana cewa ya san Sanata Marafa tun kusan shekaru 7 da suka gabata, Amma hakan ba komai bane face karairayin da ya yi don bata sunan sanatan.

“Don haka muke bukatar duk wadanda cutar sharrin 2023 ta shafe su da su daina yada karairayi su kuma bar jami’an tsaro su yi ayyukansu,” kamar yadda takardar tazo.

Labarai Makamanta