Babu Adalci Musulmi Ya Nemi Shugabancin Kasa Bayan Buhari – Kungiyar Kiristoci

Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Kungiyar Kirista ta Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, ta bukaci cewa kirista ne da dace ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023, tana mai cewa rashin adalci ne wani musulmi ya sake zama shugaba.

Shugaban kungiyar ta PFN na kasa, Bishop Francis Wale-Oke, ne ya yi wannan kiran a karshen taron kungiyar da aka saba yi duk bayan wata hudu, da wannan karon aka yi a Legas.

“Ba mu tunanin ya dace wani musulmi ya sake zama shugaban kasa a 2023 domin musulmi ya yi mulki na shekara takwas. Coci ta mara masa baya. Mun masa addu’a kuma mun bashi goyon baya. Ba mu yi nadama ba. Amma yanzu shugaban kasa kirista muke so.”

Ya kara da cewa idan aka yi nazarin yadda shugabancin kasar ke tafiya, karba-karba ake yi tsakanin musulmi da kirista tun shekarar 1999, Obasanjo, Yaradua, Jonathan sai Buhari. “Bai dace daga Shugaba Buhari sai wani musulmin ba.

Limamin Kiristan ya roki gwamnatin tarayyada ta yafe wa Nnamdi Kanu da sauransu laifukansu Shugaban na PFN ya kuma jadada kirar da kungiyar ta yi wa gwamnatin tarayya ta kira taro don tattaunawa kan manyan abubuwa biyu da ke adabar kasar da ke cigaba da jan yajin aiki da saka matasa barin kasar.

Malamin ya ce: “Ya kamata shugabannin mu su sake dagewa. Muna godiya bisa aikin da suke yi amma ya kamata su kara kaimi. Darajar naira a kasuwar duniya abin damuwa ne kuma ba mu amince da shi ba. “A dauki mataki game da tattalin arzikin kasar.

Labarai Makamanta