Babu Abin Da Zai Hanani Rufe Layuka Marasa Rijistar Ɗan Ƙasa – Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arziki na Digital Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya gargadi yan Nijeriya wadanda har yanzun ba su hada layukan wayar su da katin zama dan kasa NIN ba, da suyi gaggawar yi.

Ministan ya ce babu gudu ba ja da baya, dan haka kowa ya gaggauta hada nashi tun kafin lokaci yayi.

Ministan ya fadi hakane a wasu sakonnin da ya aike a shafinsa na kafar sada zumunta tuwita ya yin da yake martani kan karyar zargin da wasu jaridu ke masa da hannu a Boko Haram.

Ministan ya ce babu wasu yan shaci-fadi da wasu tsirarun mutane da za su mishi barazana da shi da zai iya dakatar da shi gudanar da kudirin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Labarai Makamanta