Babu Abin Da Zai Hana Zaben Gwamna A Anambra – INEC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu ya bai wa al’ummar jihar Anambra tabbacin cewa ba bu abinda zai hana zaben gwamna na ranar 6 ga wata kamar yadda hukumar ta tsara.

Ya ce INEC ta shirya tsaf don gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe.

A taron masu ruwa da tsaki da ya halarta a hedikwatar INEC da ke Awka, Farfesa Mahmood Yakubu ya bukaci jami’an tsaro da su basu hadin kai don tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin lumana.

Dama rundunar yan sandan Najeriyar ta yi alkawarin maganin duk wanda ya yi yunkurin kawo wa zaben na ranar Asabar mai zuwa cikas.

Itama kungiyar MASSOB mai fafutukar kafuwar Biafra ta ce babu wanda ya isa ya hana gudanar da zaben gwamnan.

A baya kungiyar IPOB da itama ke fafutukar ballewa daga Najeriya wadda shugabanta Nnamdi Kanu yanzu haka ke hannun hukumomi, ta yi barazanar hana gudanar da zaben.

Bugu da kari mambobin kungiyar sun rika kai hare-hare kan jami’ai da gine-ginen gwamnati har ma da saka wa al’umma dokar hana fita, wanda hakan ya saka wa wasu tsoro da shakku kan yiyuwar gudanar da zaben.

Labarai Makamanta