Babu Abin Da Mulkin Buhari Ya Tsinana Wa Najeriya – Dr Hakeem Baba Ahmed

Mai magana da yawun majalisar dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba-Ahmad ya bayyana cewa, bai dace Najeriya ta samu shugaba mai irin halayen Buhari ba, kuma dole shugaban Najeriya na gaba ya sha bamban da akidun Buhari.

Hakeem ya yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa da jaridar Punch da aka buga a ranar Lahadi 9 ga watan Oktoba na wannan shekara.

“Bana tunanin za mu tsira na tsawon shekaru goma tare idan muka ci gaba da tafiya yadda muke a karkashin Buhari.”

A bangare guda, ya bayyana tasirin matasa masu jini a jika saɓanin tsofaffi a tsakanin ‘yan siyasa, inda yace kamata ya yi Najeriya ta duba mai jini a jika kuma mai tunanin gobe domin ya gaji Buhari.

“Mutum zai iya zama matashi amma ya gaza yin komai, kuma mutum zai iya zama mai shekaru ya gaza gane menene sauyi. Ka duba shugaban kasa. Bai sauya komai ba tun daga 2015 har zuwa yau.

Labarai Makamanta