Babbar Magana: Ba Buhari Ke Mulkin Najeriya Ba – Aisha Buhari

Uwargidan Shugaban ƙasa Aisha Buhari ta ce ‘miyagun mutane’ sun karbe mulki daga hannun Mijinta da sauran mutanen da ya dace su rika ‘tafiyar da ragamar mulkin kasar’ lamarin da ya katange Shugaban daga aiwatar da muhimman ayyuka ga ‘yan Najeriya kamar yadda ya yi alkawari.

Aisha ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin hirar wayar tarho da aka yi da ita a wani shiri na Television Continental (TVC).

Ta ce bai dace wadanda ya kamata su rika tafiyar da gwamnati suyi shiru ba yayin da wasu mutane ke amfani da kafafen sada zumunta suna kokarin bata sunan gwamnati.

Ta ce labaran karya da ake wallafawa sun jefa ta cikin damuwa musamman lokacin da ake rade-radin cewa shugaban kasa ya mutu da kuma lokacin da aka ce shugaban zai kara aure.

“Ban dauke shi da muhimmanci ba saboda miji na ma bai san abinda ke faruwa ba,” ta ce game da rade-raden kara auren shugaban kasar.

“Dukkan mu ba mu san abinda ke faruwa ba; kawai sun fara yaɗa labarin ne a kafafen sada zumunta. Yanzu suna amfani da kafafen sada zumunta domin kawo karshen gwamnati.

“Ina tunanin bai dace mu kyale mutanen da ba su kai sun kawo ba su ci zalin ‘yan kasa na gari; Ban san dalilin da yasa mutanen da ya dace su dauki mataki suka yi shiru ba yayin da bata gari ke kwace kasar daga hannun mu. Ba zai yiwu ba kuma ba zamu amince da hakan ba.”

Aisha ta kuma ce hadiman shugaban kasa da sauran ma’aikatan gwamnati suna watsi da muhimman abubuwan da ya dace su dauki mataki a kai kana suna mayar da hankali kan abubuwan da bai shafi shugaban kasa ba.

Ta ce, “Duk lokacin da ya dace su (hadiman shugaban kasa) su dauki mataki kan masu aikata laifuka ko su gargadi su sai su ja bakinsu suyi shiru.”

“Amma idan abubuwan da ba su da muhimmanci ne mutane za su fara magana kan shugaban kasa. Misali shine abinda ya faru bayan zaben Bayelsa. Lokacin da PDP ta fito ta ce za ta dakatar da tsohon shugaba, Goodluck Jonathan kan aikata wani laifi ko wani abu mai kama da haka.

“Ban ga dalilin da zai sa fadar shugaban kasa ta fito ta ce tayi mamakin jin hakan ba. Matsalar su ne? Su ‘yan PDP ne? Shin Jonathan dan jam’iyyar mu ne? Mene hadin fadar shugaban da lamarin

Related posts