Babbar Kotun Tarayya Ta Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar kotun tarayya ta Abuja ta bayyana kungiyoyin `yan bindiga da ke barna a fadin kasar nan a matsayin ‘yan ta’adda.

An ruwaito cewa, Mohammad Abubukar, daraktan gurfanarwa (DPP) a ma’aikatar shari’a wanda ya shigar da karar, yace: Kotun Abuja ta ayyana ‘yan bindiga matsayin ‘yan ta’adda, bisa ga munin ayyukan su.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da matakin da aka dauka,wanda babban dalilin hakan shine ganin bayan kungiyoyin `yan bindiga da ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyin ta’addanci a kasar.”

A wata takardar karfafawa da ta fito daga gwamanatin tarayyan data kunshi rahotanni akan harkar tsaro, sun tabbatar da cewa kungiyoyin `yan bindigan ne ke da alhakin kashe- kashe, garkuwa da mutane gami da fyade da sauran munanan ayyuka a arewa maso yamma da arewa da sauran bangarorin kasar.

An zargi kungiyoyin da alhakin assasa ta’addanci, cigaba da garkuwa da mutane tare da bukatar wani kaso na dukiya, satar mata domin aure da satar yaran makaranta da sauran mutanen kasa.

A lokacin gudanar da shari’a a ranar Alhamis, kotu ta bayyana ayyukan kungiyoyin`yan bindiga da `yan ta’adda da sauran kungiyoyin da suka kunshi nau’in ta’addanci a sasanni kasar, musamman a arewa maso yamma da arewancin kasar a matsayin nau’in ta’addanci da karya doka.

Kotun ta yi Alawadai da ayyukan kungiyoyin da makamantansu a kowanne sassan kasar, ko a kungiya ko a ware da sunan koma me suke amfani da shi. Kotun ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ayyana `yan bindiga a matsayin `yan ta’adda da kan ta cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

Labarai Makamanta