Babban Zabe: Tuntuben Harshen Tinubu Ya Haifar Da Rudani

‘Yan Najeriya sun shafe tsawon lokaci suna ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta dangane da wasu kalamai ko subul-da-baka da ɗan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a wurin yaƙin neman zaɓensa.

A ranar Talata ne Bola Tinubu ya kaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen nasa a Jos, babban birnin jihar Filato, wanda Shugaba Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka halarta.

Sai dai a jawabinsa lokacin da ya hau dandamali ya yi wasu kalamai da wasu ke gani subul-da-baka ne.

Irin wadannan kalamai su ne wasu ‘yan Najeriya suka rinka watsawa a shafukan sada zumunta, wasu na amfani da kalaman zolaye, wasu kuma na cewa wannan katoɓara alamomin gazawa ce.

Kusan abu biyu ne suka ja hankalin ma’abota shafukan sada zumunta da kuma mutanen da suka bibbiya yadda gangamin ya kasance a garin Jos.

Akwai kuskure da ɗan takarar Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen kiran sunan jam’iyyarsu ta APC, inda aka jiyo ɗan takarar na ambato harufa biyu na babbar jam’iyyar adawa wato PDP, inda ya ce “PD…” amma daga bisani ya gyara ya ce “APC”.

Wannan kuskure ko subul-da-baka da Tinubu ya yi ya ja hankali sosai, inda mutane suka yanko daidai wajen suna ta sake wallafawa da takfa muhawara a kai.

Wasu ma sun haɗe sunan suna cewa ko dai Najeriya ta yi sabuwar jam’iyya ce ta “PDAPC”.

A gefe guda kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi martani kan kalaman na Tinubu inda ta bayyana su a matsayin wata ishara ce dake nuna samun nasarar PDP a babban zaɓen dake tafe.

Sannan ta yi kira ga Tinubun da cewa cikin gaggawa ya nemi gafarar ‘yan Najeriya kan abin da suka kira katoɓarar da ya tafka sannan ya gaggauta janye wa daga takarar shugabancin kasar.

Labarai Makamanta