Babban Zabe: Gwamnoni Ne Za Su Zabar Wa Tinubu Mataimaki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an yi ittifaki akan cewa gwamnonin Jam’iyyar APC ne ke da alhakin zaɓar wa zaɓaɓɓen ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Bola Tinubu wanda zai yi mishi mataimaki a zaɓen dake tafe na 2023.

Da yake magana ta kafar talabijin Trust TV a ranar Laraba, Bayo Onanuga mai magana da yawun kwamitin kamfen na Tinubu, ya ce Bola Tinubu ya yi wa gwamnonin APC alƙawarin hakan ne lokacin da ya gana da su.

“Lokacin da Tinubu ya gana da gwamnonin APC a ƙungiyarsu, ya faɗa musu cewa ku ne za ku zaɓi abokin takarata,” a cewarsa.

A ranar Laraba ne daliget daga jiha 36 na Najeriya suka kaɗa ƙuri’ar zaɓen Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar APC, inda ya doke sauran ‘yan takara 13 da suka shiga zaɓen.

Labarai Makamanta

Leave a Reply