Babban Sifeton ‘Yan Sanda Ya Raba Biliyan 13 Ga Iyalan ‘Yan Sanda Da Suka Mutu A Bakin Aiki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya fara raba cekin kudi na inshorar jami’an da suka rasa rayukansu a bakin aiki, da kuma waɗanda suka rasa wasu gaɓoɓinsu a yayin aiki.

Kudin za a raba su ne ga iyalai kimanin dubu bakwai wadanda suka rasa ‘yan uwansu ko kuma suka jikkata a bakin aiki ko wadanda suka rasa gaɓɓansu yayin aiki tsakanin shekarar 2012 zuwa 2020 wanda sun haura naira biliyan 13.

Usman Baba ya ce an bayar da kuɗaɗen ne ga waɗannan mutane domin su rike kansu, da kuma tabbatar da cewa an bayar da cikakkiyar kariya ga jami’an da suka zaɓi su kare rayuwar ‘yan Najeriya baki ɗaya.

Lokacin da yake tsokaci, Usman Baba ya ce kudin ba za su dawo da abin da aka rasa ba, amma za su kara kwarin gwiwa ga waɗanda ke cikin aiki wajen gudanar da aikinsu, tun da sun kwana da sani kasarsu ba za ta manta da su ba.

Baba ya kara da alkawarin samar da tsarin walwala mai kyau ga waɗanda suke aiki da waɗanda suka yi ritaya, domin ci gaba da samun waɗanda za su ci gaba da wannan aiki a cikin iyalansu.

A wani labarin na daban an tsawaita wa’adin babban sifeton ‘yan sandan na ƙasa.

Ministan harkokin ‘yan sanda Mohammed Maigari Dingyadi, ya ce babban sifeton ‘yan sanda Usman Baba Alkali, ba zai yi ritaya a lokacin tsakiyar zaɓukan ƙasar da ke tafe, kamar yadda ake tsammani.

Ministan na wannan maganar ne yayin da yake amsa tambayar manema labarai a fadar gwamnatin jim ƙadan bayan kammala taron majalisar zartawar ƙasar.

Dingyadi ya ce tuni babban sifeton ‘yan sandan ya karɓi takardar tsawaita aikinsa – ya ƙara da cewa sabuwar dokar aikin ‘yan sanda ta 2020 ta sauya tsarin ritayar sifeton ‘yan sandan.

Labarai Makamanta