Babban Na Hannun Daman Buhari Ya Fice Daga APC

Labarin dake shigo mana yanzu haka na bayyana cewar tsohon abokin siyasar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Rufai Hanga ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki cikin gaggawa.

Kamar yadda ya shaida, a halin da ake ciki jam’iyyar APC ba ta da wani tasiri don haka bai ga amfanin bata lokacin sa da cigaba da zama cikinta ba.

Hanga wanda babban ginshiki ne na jam’iyyar, amma yanzu ya duba ya ga babu mamora don haka ya cika wa rigarsa iska.

Hanga wanda shine shugaban jam’iyyar CPC na farko, ya sanar da jaridar The Independent cewa har yanzu bai shiga wata jam’iyyar ba.

CPC ce tsohuwar jam’iyyar shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin su yi maja da ACN da sauran jam’iyyu su hada jam’iyyar APC. A cewar Hanga, duk da ya yi aiki tukuru wurin gina jam’iyyar APC, ba zai zauna yana gani jam’iyyar ta rushe yayin da yake cikinta ba.

“Eh duk da na bar jam’iyyar APC, har yanzu ban sanar da jam’iyyar da na koma ba. Amma na bar jam’iyyar kuma ina ganin abubuwan da suke yi yasu-yasu.”

Labarai Makamanta