Babban Burina Talakan Najeriya Ya Mori Arzikin Najeriya – Buhari

Mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar babban burinshi shine Talakan Najeriya ya mori tarin arzikin Najeriya da Allah ya huwace wa ƙasar.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari na aiki tukuru dan tabbatar da alkawarin da ya dauka na ganin cewa kowane dan Najeriya ya amfana da dukiyar kasar ba tare da la’akari da inda ya fito ba.

Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya bayyana haka a Adamawa wajan kaddamar da wani aiki da ya wakilci shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

“Bisa ga tarin ayyukan alheri da Shugaban ƙasa yake ta faman yi a halin yanzu na inganta rayuwar Talakan kasar, za’a iya cewa shugaban ya dauko hanyar share hawayen talakawan kasar.

A kwanakin baya dai an ruwaito Ministan yaɗa labarai da al’adu Lai Mohammed ya fito ya bayyana cewar a tarihin Najeriya ba’a taɓa samun wani shugaba wanda ya damu da damuwar talakawa kamar Buhari ba.

Labarai Makamanta