Babban Burina Shine Tallafawa Marasa Galihu – Aisha Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bayyana cewa a shirye ta ke ta karfafa hadin gwiwa da sauran masu hannu da shuni don bayar da tallafin da ake bukata a ci gaban ilimin mata da yara.

Aisha Buhari ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, a lokacin da ta karbi bakuncin mambobin kungiyar masu harhada magunguna ta Najeriya (NAPPSA), daga kasar Amurka, wadanda suka kai mata ziyara a Abuja.

Ta ce gidauniyar ta, ta hanyar hadin guiwar abokan huldar ci gaba, ta bayar da tallafi ga mata, matasa da sauran iyalai marasa galihu, musamman a fannin kiwon lafiya, gina asibitocin haihuwa da inganta ilimin yara mata.

Uwargidan shugaban kasar ta kuma shaida wa maziyartan cewa gidauniyar Aisha Buhari ta gina kwaleji a Maiduguri da nufin tallafa wa yara mata wajen neman ilimi musamman yaran da iyayensu suka mutu a rikicin Boko Haram.

“Kafa Kwalejin Future Assured a Maiduguri, jihar Borno kwanan nan, an yi shi ne don samar da ilimi ga yara ‘yan mata wadanda rikici ya shafa. “Wannan tallafin da aka bayar shine jagorar abin da za mu iya yi tare don tallafa wa wadannan matasan don su samu kyakkyawar makoma duba da kalubalen da ke fuskantar ilimin ’ya’ya mata.

Labarai Makamanta