Babban Bankin Kasa Ya Samar Da Sauki Ga ‘Yan Najeriya

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi nazari kan kudaden da ake kashewa da kuma adadin kudaden da ake cirewa kwastomoni a harkokin bankuna a kasar inda ya samar da sauki ga ‘yan ƙasa.

Babban Bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sabuwar takardar da ya fitar mai taken Hanyoyin karɓar kuɗaɗe ga Bankuna da sauran cibiyoyin hada hadar kuɗaɗe ‘Guide to Charges by Banks Other Financial and non-Financial’.

Babban bankin ya ce hakan zai shafi dukkan bankuna da kuma cibiyoyin hada-hadar kudade a duk fadin Najeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa CBN ya rage wasu cajin da suka hada da na ‘Standing Order Charge’; Kudin Gudanar da ATM; canjawa kudi wurin zama daga asusu zuwa wani asusun da tura kudi da yawa da dai sauransu.

A cikin sabuwar ka’idar, CBN ya ce kudaden da ake cirewa na ‘Standing Order Charge’ na banki zai kasance kyauta idan aka kwatanta da N300 a cikin ka’idar 2017. Dangane da tura kudade tsakanin bankuna, CBN ya rage cajin kudi zuwa N50 a kowane ciniki idan aka kwatanta da N300 da aka bayyana a 2017.

Hakanan an sake duba tsarin tura kudi wato ‘transfer’ ta intanet zuwa kasa zuwa N10 a kan N5000; N26 a N5001 zuwa N50,000 yayin da sama da N50,000 za a caji N50. An rage farashin cire kudi daga mashunan ATM na wasu bankuna daga N65 zuwa N35 bayan cirewa na uku a cikin wata guda.

Labarai Makamanta