Babban Banki Ya Karyata Labarin Umartar Bankuna Da Karbar Tsoffin ₦1000 Da ₦500

Babban bankin Najeriya ya karyatq maganar cewa ya canza shawara kan lamarin mayar da tsaffin kudin N1000 da N500 ko wane bankuna

Dubunnan yan Najeriya sun dira ofishohin CBN yau don mayar da tsaffin kudadensu bayan jawabin Buhari.

Gwamnoni akalla 10 suka ja daga dashugaban kasa inda wasu suka fara yi masa bore

Jawabin wanda har bankuna sun fara sanar da kwastamominsu su kawo kudi ya karade kafafen
yada labarai.

Har an ruwaito Daraktan Sadarwa na bankin, Osita Nwanisobi, da tabbatar da labarin. Kusan dukkan kafafen yada labaran Najeriya sun dauki labarin.

Kwatsam Osita Nwanisobi ya fitar da sabon jawabi cewa wannan labari ba gaskiya bane bankin bai sanar da hakan ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply