Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce a yanzu al’ummar kasar za su iya ci gaba da amfanin da tsofaffin takardun kudi na naira 200, da 500 da kuma 1,000.
A wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Litinin da daddare, wadda ta samu sa hannun mukaddashin daraktan yada labarai na bankin, Isa AbdulMumin, bankin ya ce ya yi hakan ne domin jadadda bin doka irin ta gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Sanarwar ta ce, “Bisa yin biyayya ga halayyar girmama shari’a ta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, da kuma na ayyukan Babban Bankin Najeriya, an umarci bankunan ajiya da ke aiki a Najeriya su bi umurnin kotun koli na ranar 3 ga watan Maris.”
“Bugu da kari, CBN ya gana da kwamitin harkokin bankuna, kuma bayan haka ya yi umarni da a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sababbin takardun kudi na naira 200, da 500 da kuma 1,000 har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.”
“Saboda haka ana umurtar duk wadanda abin ya shafa su yi aiki da wannan umarni.”
Sanarwar dai na zuwa ne jim kadan bayan wata takarda da fadar shugaban kasa ta fitar ta nesanta shugaba Buhari da umartar Babban Bankin na Najeriya da ya bijire wa umarnin kotu a game da daina amfani da tsofaffin kudin.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ta ce ko kadan shugaban kasar ba zai umarci wani daga cikin CBN ko ministan shari’a na kasar su ki amfani da umarnin kotu ba.
You must log in to post a comment.