Babban Aikin Ku Shine Fitar Da ‘Yan Najeriya Daga Talauci – APC Ga Ministoci

Jam’iyyar APC ta shaidawa sabbin Ministocin da aka kaddamar cewa akwai fa wani mahimmin aiki da ke gabansu da ake son su hanzarta aiwatarwa na fitar da ‘yan Nijeriya daga kangin Talauci, su tsartar da rayukansu da dukiyoyinsu su kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Jam’iyyar ta kuma ce, ‘yan Nijeriya suna sauraronsu da su gina masu mahimman ayyukan raya kasa, su maido da tarbiya su kuma dawo da hamasan ‘yan Nijeriya ta hanyar bayar da misalai daga kawukansu ta yanda Nijeriya za ta yi alfahari da su.

A cikin sakon taya murna da ta aikewa Ministocin, wacce Sakataren yada labarai na Jam’iyyar na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ya sanyawa hannu, APC ta bukaci sabbin Ministocin da su zauna sosai su kuma hanzarta kama ayyukansu yanda ya kamata.

Sanarwar tana cewa, “Don haka, muna bukatar sabbin Ministocin da su tabbatar da amincewar da Shugaban kasa tare da sauran ‘yan Nijeriya suka yi masu ta hanyar zama sosai su gudanar da ayyukansu a cikin hanzari domin tallafawa nasarorin da aka samu a sassa daban-daban.

“Muna tare da Shugaban kasa wajen yin kira ga sabbin Ministocin da aka kaddamar da su tabbatar da yin aiki a tare da juna domin kyautata alaka a tsakaninsu wajen tafiyar da aikin gwamnati. Wannan ce hanya daya da za mu iya kaiwa ga manufarmu ta mataki na gaba.

“Yana kuma da mahimmanci sabbin Ministocin su fahimci cewa su fa Ministocin gwamnatin Jam’iyyar APC ce, don haka ya kamata su nuna halayya na ci gaba da dabi’u nagari.

“Jam’iyyar APC tana taya sabbin Ministoci murna da fatan samun nasara a mukamansu, tare da shugabancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, su yi aiki a tafarkin kai kasarmu zuwa ga mataki na gaba. Muna tabbatarwa da Ministocin cikakken goyon bayan Jam’iyya a gare su domin ganin samun nasararsu.

Related posts