Babban Ɗan Majalisar Masarautar Katsina Ya Rasu

Allah Ya Yi Wa Khadi Sule Sada Kofar Sauri, Wanda Ke Rike Da Sarautar Alkalin Garka Kuma Daya Daga Cikin Manyan Yan Majalisar Sarkin Katsina, Mai Martaba Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman Rasuwa.

An Haifi Alkalin Garka, Alhaji Sule Sada Kofar Sauri A Shekara 1948 A Unguwar Kofar Sauri Cikin Garin Katsina. Ya Zama Khadi A Shekarar 1995.

Babban Limamin Katsina, Liman Ratibi Ya Yi Masa Sallah Da Misalin Karfe Sha Daya Na Rana A Unguwarsu Ta Kofar Sauri A Yau Lahadi.

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman Ya Halarci Sallah Jana’izarsa Da Wasu Daga Cikin Yan Majalisar Zartaswa Da Shugabannin Hukumomin Gwamnatin Jihar Katsina.

An Rufe Shi A Makabartar Rimin Badawa Dake Filin Samji Cikin Garin Katsina.

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Labarai Makamanta