Ba Zan Taɓa Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba – El Rufa’i

Gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Nasir Ahmad El-rufa’i ta musanta labarin da ake yaɗawa cewa an naɗa wata tawaga da zata jagoranci tattaunawa da ‘yan bindiga a fadin Jihar.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Lahadi.

Ya ce gwamnatin Kaduna ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Ahmad Elrufa’i ta ji labarin ana yaɗa jita-jita a kafar sada zumunta cewa gwamnatin ta naɗa wakilai da zasu tattauna da yan bindiga a madadinta.

A jawabin da kwamishinan ya yi a madadin gwamnan ya ce: “Gwamnatin Kaduna na kara tabbatar da cewa bata naɗa kowa ba dan shiga tsakani da yan bindiga.” Duk Soki Burutsu ne, Bamu naɗa kowa dan tattaunawa da yan Bindiga ba, babu sulhu tsakanin mu da ‘yan Bindiga!.

A maganarsa ya ce gwamnatin Kaduna na nan akan bakarta na ba zata tattauna da yan bindiga ba. “Gwamnatin mu ba zata tattauna da yan bindiga ba haka kuma bazata biya kudin fansa ba.

Duk mutumin da aka kama yana haka da sunan wakilin gwamnati za’a hukunta shi kamar yadda doka ta tanazar.” a cewar kwamishinan.A Kwanakin baya dai, Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa gwamnatinsa ba zata tattauna da yan bindiga ba kuma ba zata biya wani ɗan bindiga kuɗi da sunan kuɗin fansa ba.

Labarai Makamanta