Ba Zan Bari ‘Yan Ta’adda Su Ɓata Tsarin Ilimi Ba – Buhari

Mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ko kaɗan ba zai lamunci kai hare-hare da ‘yan Bindiga ke yi a makarantu ba da nufin kassara harkar ilimi ba, gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don kare tsarin makarantun kasar nan daga ‘yan bindiga, masu satar mutane da ‘yan ta’adda da ke kokarin rusa ta.

Shugaba Buhari ya yi magana game da matsalolin da ke faruwa a kwanan nan na masu satar mutane da hare-haren ‘yan bindiga a makarantu da sace daruruwan yara ‘yan makaranta.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai Malam Garba Shehu ya fitar wadda aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja.

Shugaba Buhari ya yaba da kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi da kuma martanin sojoji na farko wanda ya kai ga kubutar da dalibai 180 da suka hada da ma’aikata takwas, amma ya bukaci sauran da aka bayyana batan su da su dawo lafiya ga dangin su.

Shugaban ya kuma yaba wa kokari da gudummawar da ake bayarwa na leken asiri domin dakile masu satar, yana mai cewa kasar da ke da ingantacciyar hanyar sadarwa ta cikin gida kasa ce mafi aminci.

“Sojojinmu na iya kasancewa masu inganci da kuma makamai amma suna bukatar kyakkyawan kokari don kare kasar kuma dole ne jama’ar gari su tashi tsaye kan wannan kalubalen na wannan lokacin,” in ji Shugaban.

Shugaba Buhari ya nuna juyayi ga wadanda wannan lamarin ya rutsa da su sannan ya yi fatan kawo karshen wahalar wadanda har yanzu ke hannun ‘yan bindigan.

Labarai Makamanta