Ba Zan Bada Kunya Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa – Yahaya Bello

Labarin dake shigo mana daga Lokoja babban birnin Jihar Kogi na bayyana cewar Gwamnan jihar Yahaya Bello, ya ba yan Najeriya tabbacin cewa ba zai taba cin amanarsu ba idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a babban zaben 2023 dake tafe.

Da yake magana a ranar Alhamis a yayin wani taron yan majalisar dokokin arewa maso gabas a jihar Bauchi, Bello ya ce ba zai taba ba yan Najeriya kunya ba saboda a kullun yana tsaye kan alkawarunsa.

Gwamnan wanda ya yi magana da yan majalisar a wayar tarho, ya kuma bayyana cewa yana da tabbacin cewa zai yi nasara a zaben sannan zai kai inda ake mafarkin zuwa, wannan babu shakka a ciki inji shi.

“A kan dukkanmu ne. game da jami’iyyarmu ne, game da Najeriya da kuma makomarmu ne. Amma da yardar Allah, da goyon bayanku da addu’o’i, na san za mu kai ga inda muke mafarkin kaiwa.

“Yakamata na kasance a nan domin na gode maku, amma bana so a ga ina karya doka a yanzu tunda ba a bude kofar fara kamfen ba. Ina so na bi doka. “Zan zo idan aka dage haramcin don yi maku magana baki da baki a wurarenku mabanbanta.

Sai dai, kakakina da sauran yan Najeriya masu nufin alkhairi suna yawo a kasar kuma suna zantawa da mutane masu muhimmanci, musamman masu ruwa da tsaki irin ku ina matukar godiya.

“Ina son daukar maku alkawarin cewa ba zan ba kowannenku kunya ba. Duba ga alakar da nake da shi da kakakin majalisar jihar Kogi, na san da izinin Allah idan na isa inda ake burin kaiwa, alakarmu za ta sake bunkasa idan na isa villa kuma na san zai isa villa a ranar 29 ga watan Mayun 2023, idan Allah ya yarda.

“Ina bukatar goyon bayanku. Ina bukatar addu’o’inku. Ina bukatar taimakonku. Ina bukatarku sosai saboda tare za mu iya ceto kasar sannan mu yi gini kan nasarorin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ina mai sake daukar alkawarin cewa ba zan ci amanarku ba. Ba zan baku kunya ba saboda ni mutum ne mai cika alkawari da yarda.”

Labarai Makamanta