Ba Zamu Lamunci Ta’addancin Dake Faruwa A Najeriya Ba – Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagora a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi kalamai cikin fushi dangane da kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi a sassan kasa.Tinubu ya bayyana cewa Nigeria ba zata yarda hakan ta cigaba da faruwa ba.

Babban dan siyasar ya bayyana hakan ne a Maiduguri yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, domin yi masa jajen kisan manoma fiye da 43 da ‘yan Boko suka yi.

A kalla manoma fiye da 48 aka bayyana, a hukumance, cewa an kashe a gonakinsu na gona Zabarmari, jihar Borno.

Da yake magana da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Borno, Tinubu ya ce ba za’a taba samun cigaba a wurin da rayukan jama’a ke fuskantar barazana ba.

Ba za’a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba a wurin da ake yanka mutane yayin da suka fita neman abincinsu ba,” a cewar Tinubu.

Tinubu ya bayyana cewa ya ziyarci jihar Borno ne domin jajantawa gwamna Zulum akan abinda ya faru.

Labarai Makamanta

Leave a Reply