Ba Za Mu Yafe Bashin Da Muke Bin Najeriya Ba – Bankin Bada Lamuni

A daidai lokacin da ɗimbin bashi ya yi wa Najeriya tarnaki a wuya, Hukumar bada Lamuni ta Duniya, IMF ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da zata yafewa bashin da take bi.

Zuwa yanzu Hukumar ta ware wasu kasashe 28 da zata yafewa bashin, inda za’a yi amfani da wasu kudi da aka ajiye na ko ta kwana wajen biyawa wadannan kasashen bashin da hukumar ke binsu.

Kasashen da aka yiwa yafiyar dai sune, Afghanistan, Benin, Burkina Faso, Burundi, Central African Republic, Chad, Comoros, Democratic Republic of the Congo, Djibouti, Ethiopia, da The Gambia. Sai kuma Guinea, Guinea-Bissau, Haiti, Liberia, Madagascar, Malawi, Mali, Mozambique, Nepal, Niger, Rwanda, São Tomé and Príncipe, Sierra Leone, Solomon Islands, Tajikistan, Togo da Yemen.

Jimullar bashin da za’a yafe musu shine dala Miliyan 238.

Wannan mataki da hukumar ta dauka na nuna da akwai sauran rina a kaba kenan dangane da makomar yawan basussukan da Najeriya ta ciyo a ‘yan shekarun nan.

Labarai Makamanta