Ba Za Mu Tilasta Yin Rigakafin Korona A Jihar Kogi Ba – Gwamnatin Tarayya

Karamin Ministan Lafiya Dakta Olorunnimbe Mamora, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta tilasta wa Jihar Kogi ko wata jiha a Najeriya karbar allurar rigakafin Korona ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a birnin tarayya Abuja dangane da shirin gwamnati na fara aiwatar da rigakafin cutar Korona.

Mamora yana mayar da martani ne ga kalaman da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi cewa ba zata sabu ba ya yi alluran rigakafin, ya kara da cewa mazauna jiharsa ba “aladu bane”.

Najeriya ta fitar da shirinta na rigakafin kamuwa da kwayar cutar a ranar Juma’a tare da kimanin allurai miliyan hudu na AstraZeneca / Oxford ta Korona.

An yi wa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo rigakafin cutar a ranar Asabar don nuna lafiyar allurar.

Gwamnonin jihohi suma sun fara yin alluran domin karfafa gwiwar jama’ar Jihohin su na aminta da alluran wadda ta samu karɓuwa a faɗin duniya gaba ɗaya.

Da aka tambaye shi a ranar Talata ko Gwamnatin Tarayya za ta bai wa Jihar Kogi allurar rigakafin ganin abin da gwamnan ya ce, Ministan ya ce, “Dole ne mu auna duk abin da ke ciki. Ba za mu tilasta wa kowa ya yi allurar ba.

Muna kuma sane da gaskiyar cewa har zuwa yanzu, ba mu da isassun allurar rigakafin. “Don haka, a takaice, idan wata jiha ta hanyar gwamna ko ta wani mutum da ke da wani mukami ya ce ba a son allurar rigakafin a jihohinsu, ba za mu tilasta hakan ba.

“Babbar alkiblarmu zata tafi ga jihohin da suke so kuma suke a shirye kuma har ma suka gabatar da bukatar yin alluran. “Ko da Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Ka tambaya kuma za a baka’. Za mu ba wa jihohin da suka nemi hakan. Idan wata jiha ta yanke shawara ba za ta nemi hakan ba, ba za mu tilasta wa jihar ta nemi hakan ba.”

Labarai Makamanta