Ba Za Mu Rungume Hannu Muna Kallon Ana Kisan ‘Yan Najeriya A 2022 Ba – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta rungume hannu tana kallon ƴan bindiga suna ci gaba da kisan jama’a a sabuwar shekarar da aka shiga ba.

Shugaban ya ce da yawan ƴan bindigar na miƙa wuya ga dakaru a halin da ake ciki, kuma an samar da tsare-tsare da za su ba su damar ci gaba da yin hakan a wurare daban-daban’.

A sakonsa na barka da arziƙin shiga sabuwar shekara, shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ba da himma ga bangaren fasahar zamani don sama wa matasan ƙasar abun yi, da kuma bunkasa tattalin arziƙi.

“Rashin tsaron da ake fama da shi a wasu sassan kasar nan na iya yin barazana har jama’a su kasa ganin irin nasarorin da aka samu a zahiri a fannin tattalin arziki da kuma manufar gwamnati ta sanya al’ummar kasar nan a kan turbar da ta kamata, amma ina son in tabbatar muku cewa za mu ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan alkawuranmu kuma za mu ci gaba da aiwatar da shirye-shiryenmu da tsare-tsarenmu,”.

Labarai Makamanta