Ba Za Mu Lamunci Siyasar Dabbanci A Kano Ba – Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya gargaɗi ƴan siyasa da magoya bayan su da su tabbata sun ja kunnen magoya bayansu a lokacin Kamfen, domin gwamnati ba za ta yi kasakasa ba wajen hukunta duk wanda aka samu ya na ruruta wutar tashin hankali.

Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi ga dubban magoya bayan jam’iyyar APC da suka tattaki a jihar ranar Lahadi.

Babban ɗan ɗan takarar shugaban kasa na APC Seyi Tinubu tare da ɗan gwamna Ganduje sun ja zugar dubban magoya bayan APC a cikin garin Kano inda duka yi tattaki har zuwa gidan gwamnati.

Ganduje ya kara da cewa wannan gwamnatin Kano zata ta tabbatar an yi zaɓe cikin kamala da natsuwa.

” Nan ba da jimawa ba zan gayyaci ƴan takaran gwamna na jam’iyyu duka su zo gidan gwamnati mu ci abincin rana, mu kuma tattauna.

” Wannan karon ba zan lamunci duk wanda ya nemi tada zaune tsaye ba a lokacin zaɓe ba. Kowa ya koma ya ja wa mabiya da magoya bayan sa kunne. Burin mu shine ayi zaɓe cikin kwanciyar hankali da natsuwa.

Dubban mutane ne suka fito manyan tituna domin nuna goyon bayan su ga jam’iyyar APC da kuma takarar Bola Tinubu a jihar Kano ranar Lahadi.

Labarai Makamanta