Ba Za Mu Lamunci Duk Wani Yunkurin Dakile Babban Zabe Ba – Dattawan Arewa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta gargadi wasu mutane da ke shirin yin katsalandan kan zabe da mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin lumana su shiga taitayinsu.

Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF ta ce ta yi nazarin mawuyacin halin da yan arewa da sauran yan Najeriya ke rayuwa a yanzu, da kuma damuwa da ake kan tsaro yayin zaben da za a yi a watan Fabarairu da Maris din wannan shekarar.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun direktan watsa labarai na kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed, Dattawan sun ce akwai kananan maganganun cewa ba za a yi zabe ba, kuma za a kakabawa yan Najeriya wani tsari wanda ba bisa kan zabe ba bayan Maris din wannan shekarar.

“Suna cewa wahalhalu da rashin tsaro, tsadar rayuwa, karancin man fetur, sauya tsaffin kudi don sabbi da wasu abubuwa za su shafi talakawan Najeriya kuma da gangan suna son tunzura su don kawo matsala ga zabe ko barazanar rashin yin zaben.

“Kungiyar ta ce babu dalilin da zai sa ta goyi bayan hakan. Kuma ta gargadi duk wasu masu nufin kawo cikas ga sahihin zaben da mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin lumana.

“Tabbas matsin tattalin arziki da wahalhalun da yan Najeriya ke fuskanta barazana ne ga zaman lafiya da tsaro. Dole a nemi hanyar inganta tsaron mutane da kasa. Dole a kawar da karancin man fetur baki daya.”

“Tsarin sauya kudi bai tafi yadda aka shirya ba, kuma yana kawo cikas ga kasuwanci tare da jefa mutane cikin matsi. A sake duba abin, musamman wa’adi da yadda CBN da sauran bankuna ke aiki. “Duk wani amfani da ya ke da shi, ba zai zama mai alfano ba idan ya lalata tattalin arziki, ko ya jefa talakawa cikin wahala”.

Labarai Makamanta