Ba Za Mu Iya Biyan Ma’aikata Cikakken Albashi Ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ta ce ba zata iya cigaba da biyan ma’aikatan Jihar cikakken albashi ba kamar yadda yake a tsare, bisa ga haka ba zai yiwu ta biya ma’aikatan jihar cikakken albashin su na watan Maris ba.

Gwamnatin Kanon ta bakin kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya jingina haka da saukar kuɗin da suke samu daga gwamnatin tarayya da matsalar tattalin arzikin kasa da ake fuskanta.

Kwamishinan ya kara da cewar kason da gwamnatin jihar ke karɓa daga gwamnatin tarayya ya sauka, wanda bayan nazari akansa suka gano zai yi matuƙar wahala gwamnatin jihar ta iya biyan sabon tsarin albashi.

Sai dai, duk da haka ƙungiyar ƙwadago ta jihar (NLC) ta baiwa gwamnatin wa’adin kwanaki bakwai ta maida ma ma’aikatan ragowar albashin su, kamar yadda ya ke a tsare.

Kuma Ƙungiyar kwadagon ta bayyana rage kuɗin albashin ma’aikatan da gwamnatin ta yi da cewa ya saɓa ma doka. Shugaban kungiyarreshen jihar ne ya bayyana bada wa’adin jim kaɗan bayan wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki da ƙungiyar suka yi.

Shugaban ya ce, matuƙar gwamnatin bata dakatar da wannan rage albashin ba har wa’adin ya kare, to ma’aikatan zasu tsunduma yajin aikin gargaɗi na kwana uku.

Da yake maida martani kan lamarin, kwamishinan yaɗa labaran jihar ya ce, shiga yajin aikin bazai warware matsalar ba. Malam Garba ya ce, a watan maris gwamnatin jihar ta karɓi N12,400,000,000 daga asusun gwamnatin tarayya ne.

A cikin waɗannan kuɗaɗen akwai N6,100,000,000, kason gwamnatin jihar da kuma N6,300,000,000 kason kananan hukumomi 44 da jihar ke da su.

Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnatin jihar na buƙatar ƙarin biliyoyin nairori kafin ta iya biyan Albashin ma’aikatan jihar, wanda a yanzun babu kuɗin da za’a ƙara ɗin.

A cewar kwamishinan, taron da suka yi da ƙungiyar ƙwadugon jihar a watan Mayun shekarar data gabata, sun cimma matsayar biyan ma’aikata albashi bisa yadda jihar ta samu daga asusun ƙasa.

Ya kuma yi kira ga ƙungiyar ƙwadagon da kuma sauran ma’aikatan jihar da su nuna goyon bayansu don cigaba da gina kyakkyawar alaƙa tsakaninsu da gwamnati.

Daga ƙarshe, kwamishinan ya tabbatarwa da ma’aikatan jihar cewa zasu cigaba da samun cikakken albashinsu da zarar wannan matsalar ta kauce.

Labarai Makamanta