Ba Za Mu Iya Biyan Albashi Ba – Gwamnatin Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya ce gwamantinsa ba za ta iya biyan mafi karancin albashi ba.

Yace yanzu gwamnatinsa na fama da biyan bashin da suka gada daga gwamnatin da ta gabata, na biyan albashi da kuma tafiyar da gwamnati ba ki daya.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, gwamnan ya fadi hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya yi buda baki da mambobin kungiyoyin ‘yan kwadago 36 karkashin shugabancin NLC a Gusau babban birnin Jihar.

An tabbatar da sabon mafikarancin albashi a Najeriya a matsayin doka a 2019 karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Kuma dokar ta yi bayanin kara kudin ne daga naira 18,500 zuwa naira 30,000.

“Zamfara wacce na daya daga cikin jihohin da suke karbar mafi karancin kudade daga gwamnatin tarayya ko wanne wata, ana cire mata sama da naira biliyan 1.6 daga kudin a matsayin bashin da ta gada daga gwamnatin baya” in ji Matawalle.

“A kowanne wata ana barin jihar da kudin da ba su wuce naira biliyan 1.8 kuma tana biyan naira biliyan 1.3 ga ma’aikatanta 28,000.

Labarai Makamanta