Ba Za Mu Iya Ba: Ku Samar Da Tsaro Ga ‘Ya’yanku A Makarantu – Buhari Ga Iyaye

Gwamnatin Tarayya ta jaddada bukatar ‘yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan don kawo karshen hare-hare a makarantu da sace dalibai.

Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, wanda ya bayyana hakan a cikin wata hira da jaridar The Punch a ranar Litinin, ya nuna cewa gwamnati ba za ta iya tabbatar da tsaron kowace makaranta a kasar ba.

A cewarsa, gwamnati ta umarci makarantu su kai rahoton duk wata barazanar tsaro ga hukumar tsaro mafi kusa.

A cikin tattaunawar, an tambayi ministan abin da gwamnati ke yi don kare makarantu daga hare-haren ‘yan bindiga.

Ya amsa da cewa, “Kulawa ta din-din-din itace farashin tsaro. Kowace kasa tana da damuwa a ko yaushe game da wayewar jama’arta.

“Gwamnatin Tarayya ba za ta iya tsare kowane gida ba. Kowa na bukatar yin ta kansa.

Mun isar da wannan sakon ga dukkan makarantunmu ta yadda a duk inda suke, idan akwai wata barazana, to su sanar da hukumar tsaro da ke kusa da su.”

Nwajiuba ya kuma yi ikirarin cewa kusan duk makarantun kasar nan suna shinge.

“Kusan dukkan makarantun da ke Najeriya, ko masu zaman kansu ne ko na Gwamnatin Tarayya, galibi duk suna da shinge, sai dai watakila wasu makarantun jihohi.

“Kamar yadda kuma ku ka sani, ko da kun sanya shinge, wadannan mutane (‘yan bindiga) an san su da zuwa su kutsa ta kofofi.

“Don haka, shingen kewaye makarantu, da kansu, ba su da tasiri sosai. Matakin tsaro shine abinda ake bukata.

“Idan kun ji inda ake tsare da wasu daga cikinsu, za ku san cewa tambaya ce ta sanin kai da kuma al’ummomin da ke sanar da jami’ai a kan lokaci.”

Labarai Makamanta