Ba Za A Daina Kashe ‘Yan Arewa A Mulkin Buhari Ba – Shugaban Matasan Arewa

An bayyana cewar wata dama ce mutanen Kudu suka samu har suke kisan kiyashi akan ‘yan Arewa a Jihohin su, saboda imanin da suke da shi cewa babu abin da zai faru domin sun yi kisan a karkashin Mulkin Buhari, saboda rashin martaba rayukan ‘yan Arewa da gwamnatin Buhari ke yi.

Shugaban gamayyar kungiyoyin cigaban Arewa Alhaji Nastura Ashir Sherif ya bayyana hakan, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Kaduna dangane da halin da jama’ar Arewa suka tsinci kansu na kisan da ake yi musu yanzu haka a sashin Kudancin Najeriya musamman Jihohin Yarbawa.

Ashir Sherif ya ƙara da cewar ko kaɗan wannan gwamnati ba ta ɗauki rayuwar ɗan Arewa a bakin komai ba, abin da kawai aka ɗauki ɗan Arewa shine gugar yasa wanda amfaninsa kawai ya fito lokacin zaɓe ya jefa ƙuri’a, a haye madafun iko a bar shi a rana.

Shugaban gamayyar kungiyoyin Arewan ya cigaba da cewar da gangan ne aka bari harkar tsaro ta lalace a Arewa saboda amfana da hakan da ƙusoshin gwamnati ke yi da harkar, sannan a duk lokacin da aka samu wani mutum ya fito da niyyar shawo kan matsalar sai a nemi wani sharri a jefe shi dashi.

Ya bada misali da kokarin da sanannen malamin nan Dr.Ahmad Gumi ke yi na ganin an shawo kan matsalar tsaro a yankin Arewa, amma abin mamaki da takaici maimakon a yaba mishi ko a goya mishi baya, sai ya zamana an fito ana ta sukar shi.

“Kowa ya ga irin cin zarafin da shugaban tsagerun Yarbawa Sunday Igboho ke yi, na jagorantar Zanga-Zangar kisan ‘yan Arewa a Kudu ba tare da samun wata turjiya ba, amma a lokacin da Matasa a Arewa suka shirya gudanar da Zanga-Zanga ta Lumana akan jan hankalin Gwamnati na taɓarɓarewar tsaro a Arewa, nan take jami’an tsaro suka daƙile shirin, sannan aka yi amfani da Malaman Addini suka hau mimbari suna faɗin wai babu Zanga-Zanga a cikin Addini”.

Nastura Ashir Sherif ya bayyana cewar ɗan Arewa ya sani kuma ya daina yaudarar kanshi wannan gwamnati ta Buhari ba ta da wani shiri na kare rayuwar shi, kuma lallai ne rayuwar ɗan Arewa na cikin hatsari a wannan gwamnatin, domin waɗanda suke rike da ragamar tsaro a ƙasar duk da kasancewar su ‘yan Arewa ba Arewa ce a gaban su ba.

Labarai Makamanta