Ba Za A Binciki Wadanda Suka Sayi Fom Miliyan 100 Ba – Fadar Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaban kasar ba zai binciki yadda yan takara suka samu kudaden da suka kashe wajen siyan fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba.

Mallam Garba Shehu ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin Channels TV a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu.

Shehu ya bayyana cewa aikin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da kungiyoyin jama’a ne gano yadda aka yi suka samu wannan kudi ba wai aikin shugaban kasa ba.

“Tambayar shine ya aka yi suka samu naira miliyan 100 suka sayi fom? Ina ganin ya kamata tambayar ta je ga kowane dan takara ne. Irin wannan bincike ya rataya ne a wuya kungiyoyin jama’a sannan kafafen yada labarai su rika yin tambayoyi, amma suna cewa shugaban kasa ya yi bincike, ba na tunanin wannan ne mafita.

Labarai Makamanta