Ba ‘Yan Bindiga Bane Suka Kashe Kwamishina A Katsina – Masari

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan kashe kwamishinan kimiyya da fasaha, Dakta Rabe Nasir, ranar Laraba, gwamnan Katsina, Aminu Masari a Abuja, yace kisan ba shi da alaƙa da yan bindiga.

Gwamnan na cewa ya zama wajibi baki ɗaya jihohin arewa ta yamma su haɗa karfi da ƙarfe wajen magance ƙalubalen tsaro da ya addabi yankin.

Masari ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labarai na gidan gwamnati ranar Talata, bayan ya jagoranci tawagar dattawan Katsina sun sa labule da shugaba Buhari a Abuja.

“Lamarin da ya faru makon da ya shuɗe ba shi da alaƙa da harin yan bindiga, wasu masu kisan gilla da ba’a gano su ba ne suka kashe shi.” “Kuma a halin yanzun jami’an yan sanda da sauran hukumomin tsaro na aiki ba dare ba rana domin gano abinda ya faru.

Kwamishina na ya rasa ransa a hannun masu kisan gilla kuma ba su ɗauki komai ba a gidansa.” “Saboda haka wannan wani babban laifine dake bukatar a tsananta bincike domin mu gano asalin makasan da kuma dalilin kashe shi.”

Masari ya tabbatar wa iyalan mamacin da kuma mutanen jihar cewa hukumomin tsaro sun dukufa bincike domin gano masu hannu a kisan gillan.

Labarai Makamanta