Ba ‘Yan Bindiga Bane Suka Kai Hari Jirgin Kasan Abuja – Shugaban Jiragen Kasa

Shugaban Hukumar Zirga-Zirgar Jiragen Ƙasa a Najeriya ta Nigeria Railway Corporation (NRC), Fidet Okhiria ya musanta rahotannin cewa ‘yan fashi ko ‘yan ta’adda ne suka kai wa jirgin Abuja-Kaduna hari.

Sai dai Mista Okhiria ya tabbatar wa Daily Trust cewa ‘yan daba ne suka kai harin har ma suka lalata wani ɓangare na layin dogon.

“Gaskiya ne an lalata wani ɓangare na layin dogonmu,” in ji shi. “Amma ba zan iya tabbatarwa ba ko ‘yan ta’adda ne suka kai harin.”

“Layin dogon ya samu matsala kuma muna aikin gyaransa. Muna yunƙurin dawo da zirga-zirga kuma zuwa nan da daren yau (Alhamis), ya kamata mu ci gaba da aiki.”

Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta ya nuna yadda ƙarafan layin dogon ya kakkarye yadda jirgin ba zai iya bi ba.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne Laraba da dare da kuma safiyar Alhamis, inda wasu ‘yan bindiga suka buɗe wa ɓangaren direba wuta.

Labarai Makamanta