Ba Sanusi Ya Sa Na Cire Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati Ba – El Rufa’i

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya karyata rade-radin cewa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ne ya yi tasiri a kan sauye-sayen da yayi a majalisar zartarwa ta jihar.

El-Rufai ya sanar da sauye-sauye a majalisarsa a ranar 12 ga watan Oktoba a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar wadda aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.

A cikin sauye-sauyen, gwamnan ya nada sabbin mukamai ga wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatin jihar, da yin wasu manya manyan sauye sauye a majalisar zartawar Jihar.

Mista Adekeye ya ce an yi sauye-sauyen ne domin tabbatar da aiki mai kyau da ci gaban gwamnati da jihar Kaduna baki daya.

Sai dai wasu da dama sun ce tsohon sarkin Kano Sanusi ne ya yi tasiri a kan sauye-sauyen da aka yi, inda suka ba da misali da kalaman da ya yi a wani taro bayan da shugaban ma’aikatan gwamnan, Mohammed Abdullahi ya kira shi da tsohon sarkin Kano.

Da yake mayar da martani bayan mintuna kadan a taron da aka yi a Kaduna a watan Oktoba, Sanusi bai ji dadin maganar ba. A lokacin Sanusi ya ce: “Lokacin da na ji shugaban ma’aikata… Zan kira shi tsohon shugaban ma’aikata… za ku fahimci dalilin da yasa na kira ka ‘tsoho’ daga baya.”

Kwanaki kadan sai El-Rufai ya sanar da sauye-sauye a majalisarsa, inda ya tura Muhammad Sani Dattijo zuwa ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare a matsayin kwamishina.

Bayan sukar da aka yi ta yi kan tsohon sarkin bayan da El-Rufai ya sauya matsayin tsohon Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin, Sanusi ya fitar da wata sanarwa cewa kalaman da ya yi kan maganar Abdullahi a kan wasa ne. Ya ce ba shi da masaniya ko hannu a sauyin da El-Rufai ya yi a majalisar kwamishinoninsa.

Labarai Makamanta